Najeriya

Wamakko da Bafarawa sun yi cacar-baka gaba da gaba

Wamakko da Bafarawa
Wamakko da Bafarawa Facebook

Tsoffin gwamnonin jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun yi yakin cacar-baka gaba da gaba a filin jiragen sama na Sultan Abubakar na uku da ke jihar.

Talla

Rahotanni sun ce, Bafarawa ya fusata biyo bayan kalaman da Wamakko ya furta, inda yake bayyana Bafarawan a matsayin dan ci-rani a jihar.

Wannan ne ya sa Bafarawan ya ki amsa gaisuwar da Wamakko ya yi masa a yayin da suka hadu a filin jirgin saman a ranar Litinin.

A maimakon amsa gaisuwar, Bafarawa ya fada wa Wamakko cewa, “ ka ce, ni dan ci-rani ne a Sokoto, me ya sa kake gaishe ni? Na san cewa, an haifi mahaifina da kakana a nan kuma sun mutu a nan. Zan iya nuna maka kaburburansu. Za ka iya nuna min kabarin kakanka? “

Sai dai Wamakko ya ki mayar masa da martani, amma ya tsaya kan bakarsa cewa, Bafarawa dan ci-rani ne.

A cewar wamakko, “ ba na bukatar sanin inda aka binne mahaifinka da kakanka, abin da na sani shi ne, kai dan ci-rani ne a Sokoto..

Kodayake tsoffin gwamnonin biyu sun shiga jirgi guda zuwa birnin Abuja.

Wamakko dai ya yi wa Bafarawa mataimakin gwamna har kusan shekaru 8 kafin daga bisani ya yi murabus don kashin kansa domin kauce wa tsigewa.

Wamakko ya gaji Bafarawa a kujerar gwamna bayan ya yi nasarar doke Alhaji Muhammadu Mai Gari Dingyadi, dan takarar da Bafarawa ya mara wa baya a zaben 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.