Najeriya

Kotu ta dakatar da Ganduje daga kafa majalisar sarakuna

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government

Wata babbar kotun Kano da ke Najeriya ta umarci gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da ya dakatar da shirinsa na kafa majalisar sarakuna a sabbin masarautun da ya kirkiro.

Talla

Kotun ta bai wa gwamnan Ganduje umurnin kauce wa daukar duk wani mataki kan Masarautar Kano ba tare da tuntubar makusantan Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ba.

Alkalin kotun Ahmed Badamosi ya bayar da wannan umurnin sakamakon bukatar haka da wasu masu rike da mukamin a Masarautar suka shigar, wanda ya bukaci gwamnan da kada ya dauki wani mataki a karkashin sabuwar dokar Masarautun Kano da Majalisar dokokin jihar ta amince da ita, ba tare da tuntubar wadanda suka shigar da karar ba.

Rahotanni sun ce, 4 daga cikin masu nada Sarkin Kano a karkashin jagorancin Madakin Kano, Yusuf Nabahani suka shigar da karar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.