Najeriya

Mamman Daura ne ya hana a ba ni mukami- A'isha Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da matarsa A'isha Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da matarsa A'isha Buhari Liberty

Uwargidan shugaban Najeriya A’isha Buhari ta zargi Alhaji Mamman Daura da yin gaban kansa wajen bayar da umarni da yawun fadar shugaban kasa ba tare da sanin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Talla

Tun a cikin watan Oktoba ne tsamin dangantaka ya tsananta tsakanin iyalan Mamman Daura da A’isha Buhari bayan ta dawo daga balaguron watanni biyu daga Turai.

Wani faifan bidiyo da aka yada a shafun sada zumunta a kwanakin baya, ya nuna yadda uwargidan shugaban ke tayar da jijiyoyin wuya a gaban ‘yar Mamman Daura, wato Fatima saboda kulle wata kofa a fadar shugaban kasa.

A wata wasika da ta sanya wa hannu da kanta wadda kuma ta aika wa Jaridar Daily Trust a wannan Larabar, A’isha ta ce, Mamman Daura ne ya bayar da umarnin soke ofishin ‘matar shugaban kasa’ inda ya yi amfani da Garba Shehu, mai magana da yawun fadar wajen yayata wannan umarnin.

A cewar A’isha, “Garba Shehu ya wuce gona da iri” tana mai cewa, umarnin ya tozarta shugaba Muhammadu Buhari.

A’siha ta zargi Shehu da kauce wa gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa, yayin da ya karkata hankalinsa wajen hidimta wa wani bangare da ta ce, yana amfani da shi wajen cimma miyagun manufofinsa.

Uwargidan ta ce, kamata Garba Shehu ya yi murabus cikin gaggawa saboda ya wuce iyakarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.