Najeriya

MDD tayi tur da kisan jami'an agaji a Najeriya

Wasu ma'aikatan agaji a arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu ma'aikatan agaji a arewa maso gabashin Najeriya. Audu Ali Marte/AFP

Majalisar dinkin duniya, da shugaban Najeriya Muhd Buhari sun yi Allah-wadai da kisan jami’an agajin da masu tada kayar baya suka yi a arewa maso gabashin kasar.

Talla

Kungiyar agajin kasar Faransa ta Action Against Hunger dake ayyukan jin kai a Najeriyar, ce ta soma bayyana cewar ‘mayakan sun halaka mutane hudu da suka yi garkuwa da su ranar 18 ga watan Yuli.

Kungiyar ta ce uku daga cikin wadanda aka hallakan, ma’aikatanta da suka hada da Direba guda da jami’an jinkanta 2.

Kungiyar dai ba ta kira sunan Boko Haram ko ISWAP a matsayin wadanda suka aikata kisan ba, ta dai bayyana makasan a matsayin 'yan ta'adda.

Wata kididdiga da kungiyar agajin ta Action Against Hunger ta fitar a baya bayan bayan, ta ce yanzu haka tana baiwa akalla mutane dubu 300 da rikicin Boko Haram ya tagayyara a arewa maso gabashin Najeriya, tallafin abinci da magunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI