Najeriya

Boko Haram ta wallafa sabon bidiyon wadanda tayi garkuwa da su

Wani Malamin kwalejin ilimin Gashua dake Najeriya Bitrus Bwala tare da wasu mutane 10 da kungiyar boko haram tayi garkuwa da su, sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta yiwa Allah, ta kubutar da su daga hannun kungiyar.

Hoton 'yan bindiga ( domin misali kawai ).
Hoton 'yan bindiga ( domin misali kawai ). Jakarta Globe
Talla

Wani faifan bidiyo mai tsayin minti guda da rabi da kungiyar book haram ta yada, ya nuna malamin da wadanda akayi garkuwa da su suna cewa su akasarin su kiristoci ne daga Jihar Yobe, kuma suna bukatar kungiyar kiristocin Najeriya ta taimaka wajen kubutar da su.

Bwala yace an kama shi ne ranar 27 ga watan Nuwamban wannan shekara, lokacin da yake hanyar zuwa wurin aikin sa.

Malamin yace sun shaida lokacin da mayakan boko haram suka kashe ma’aikatan agaji guda 4 ranar juma’ar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI