Najeriya-Kano

Sarkin Bichi ya tsige Hakimin Dambatta

Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero, ya tsige Hakimin karamar hukumar Dambatta Muhktari Adnan, dake jihar Kano a Najeriya.

Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero tare da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero tare da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje. YouTube
Talla

Hakimin na Dambatta da aka tsige, shi ne mamban majalisar masu dana Sarki a masarautar Kano mafi dadewa, wanda kuma yana daga cikin wadanda suka zabi tsohon Sarkin jihar ta Kano marigayi Ado Bayero, tare da nada shi a shekarar 1963.

An dai nada Adnan a matsayin Hakimin Dambatta kuma Sarkin Bai na Kano ne a shekarar 1954.

Rahotanni sun ce korar Sarkin Ban mai shekaru 93 a duniya nada nasaba da biyayyar da yake yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da kuma adawar sa da kirkiro sabbin masarautu a Jihar Kano.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar Masarautar Karaye ta kori Hkimin Kiru, Ibrahim Hamza da kuma Hakimin Rimin Gado, Shehu Muhammad daga mukaman su.

Mai Magana da yawun Masarautar Karaye Haruna Gundumawa yace Masarautar ta sanar da nada Auwal Muhammad a matsayin sabon Hakimin Rimin Gado, Magajin Rafin Karaye, yayin da aka nada Alhaji Garba Alhaji a matsayin Hakimin Kiru kuma Danmadamin Karaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI