Najeriya-Kano

Kotu ta kori karar tuhumar Ganduje da laifin karbar na goro

Rahotanni daga Kano a Najeriya sun ce babbar kotun kasar ta kori karar da ake tuhumar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, da laifin cin hanci da rashawa, saboda rashin gamsassun hujjoji.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. kanostate.gov.ng
Talla

Wani lauya mai zamansa dake Kano Bulama Bukarti ya shigar da karar gaban babbar kotun, inda ya bukaci baiwa hukumar EFCC damar bincikar Gwamnan saboda karbar cin hanci daga wani dan kwangila.

Cikin shekarar bara Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo dake nuna Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hancin dala miliyan 5 daga hannun wasu ‘yan kwangila.

Bidiyon dai ya janyo ce-ce-kuce da musayar kalamai, inda gwamnatin Kanon ta zargi editan jaridar ta Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar da yunkurin bata sunan Ganduje ta hanyar wallafa biyon da bashi da sahihanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI