Za mu bai wa Buhari izinin karbo bashin Dala biliyan 30-Lawan
Wallafawa ranar:
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa, Majalisar za a amince da bukatar shugaba Muhammadu Buhari ta karbo rancen Dala biliyan 30.
A yayin zanta wa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Sanata Lawan ya ce, Majalisa ta takwas wadda ta gabata, ta ki amincewa da bukatar Buhari ne saboda rashin gabatar mata da cikakkun bayanai a wancan lokaci.
Shugaban Majalisar ya ce, yanzu bangaren zartaswar ya koyi darasi, inda a wannan karo ya gabatar da wasikarsa dauke da cikakkun bayanan ciyo bashin.
Gwamnatin Buhari ta ce, za ta ciyo bashin makudaden kudaden ne domin gudanar da wasu manyan ayyuka a sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu