NFF zata kashe Naira biliyan 7 da miliyan 500 a 2020
Wallafawa ranar:
Hukumar Kwallon kafa ta Najeriyar ta ware dala miliyan 193 wato Naira biliyan 7 da miliyan 500, a matsayin kudaden da zata kashe a shekara mai zuwa, inji jaridar wasanni ta Sports Extra.
Jaridar tace, hakan ya fito fila ne, a rahoton karshe bayan babban taron shekara-shekara na hukumar NFF a garin Benin ranar Talata, inda ta amince da bayanan kasafin kudin shekarar da ta gabata ta 2018, kuma ta gabatar da sabon kasafin kudi na shekarar 2020 mai kamawa.
A shekara mai zuwa, Najeriya za ta shiga jerin wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2022 da kuma wasannin sharen fagen cin Kofin Kasashen Afirka na shekarar 2021.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu