Super Eagles ta ci gaba da rike matsayin ta na 31 a Duniya

Tawagar kwallon kafar Najeriya Super ta ci gaba da rike matsayin ta na taka leda a duniya wato na 31 a kiyasin wata – wata na hukumar kwallon kafar Duniya FIFA.

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles Ripples Nigeria
Talla

Kamar yadda hukumar FIFA ta wallafa a shafinta na intanet, Najeriya ta ci gaba da rike matsayinta ne, da maki 1, 493 kamar yadda yake a watan Nowamba.

Wannan makin ya kuma ajiye kungiyar ta Super Eagles a matsayin na 3 a Nahiyar Afirka, biye da kasashen Senegal da Tunisia.

Tawagar kwallon kafa ta Belgium ta ci gaba da zama ta daya a duniya karo na biyu a jere a matakin wadan da ke kan gaba a fagen kwallon kafa a duniya.

Belgium wadda ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020, ta lashe dukkan wasanni 10 da ta buga a shekarar a wannan shekara.

Yayin da kasar Faransa dake rike da kofin duniya ta ci gaba da zama ta biyu a duniya, Brazil na amatsayi na uku, sai Ingila a matsayi na hudu.

Ga jerin kasashe 20 da suka fi saura taka leda a duniya.

1 Belgium
2 France
3 Brazil
4 England
5 Uruguay
6 Croatia
7 Portugal
8 Spain
9 Argentina
10 Colombia
11 Mexico
12 Switzerland
13 Italy
14 Netherlands
15 Germany
16 Denmark
17 Sweden
17 Chile
19 Poland
20 Senegal

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI