Boko Haram ta kasshe sojin Najeriya 6 a Borno

Sojin Najeriya dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas
Sojin Najeriya dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas REUTERS/Warren Strobel

Majiyar tsaro a Najeriya ta tabbatar da farmakin da tsagin mayakan Boko Haram masu biyayya ga kungiyar IS, ISWAP ta kaddamar tare da hallaka Sojin kasar 6 a yankin arewa maso gabas.

Talla

Majiyar ta bayyana cewa mayakan na ISWAP sun farmaki jerin gwanon motocin Sojin da ke kan hanyarsu gab da kauyen Tungushe mai nisan kilomita 22 da Maiduguri fadar mulkin jihar Borno.

A cewar majiyar ilahirin soji 6 da ke mota guda ne suka rasa ransu yayinda ‘yan ta’addan 3 suma suka rasa rayukansu .

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar dake biyayya ga IS suka kashe mutane 6, kana suka yi awon gaba da wasu 5, a arewa maso gabashin Najeriyan, bayan sun datse wata babbar hanya, suka kuma rika zaben jami’an tsaro da ma’aiaktan agaji, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

AKalla mujahidan kungiyar IS reshen Afrika ta yamma su 30 ne suka karbe iko da babbar hanyar da ke kusa da kauyen Gasarwa, daga arewacin babban birnin jihar Bornon Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI