Bakonmu a Yau

Dakta Musa Mohammed Maitakobi, shugaban masu motocin sufurin Najeriya kan umurnin shugaban 'yan sanda

Sauti 03:14
Jami'in dan sandan Najeriya
Jami'in dan sandan Najeriya AFP

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najariya Mohammed Adamu ya gargadi jami’ansa da kada su tirsasawa matafiya a wannan lokaci na bukukuwa kirsimati da sabuwar shekara da ake samun yawaitan matafiya a kan hanyoyin kasar.A cewar Sufeto-Janar din za’a rika sa idanu sosai da hukunta ‘yan sanda dake karban rashawa a kan hanyoyin kasar.Kan haka Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Musa Mohammed Maitakobi, shugaban masu motocin sufuri na kasar kan yadda suke ganin wannan sanarwa.