Kano

Gwamnatin Kano ta yanke hulda kai tsaye da Sarki Sunusi

Sarkin Kano Alhaji Sunusi Lamido Sunusi tareda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Sarkin Kano Alhaji Sunusi Lamido Sunusi tareda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Dandago RFI

A Najeriya, rashin jituwa tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje na kara fitowa fili, ganin har ta kai mahukuntan jihar sun sake gindaya masa wasu sabbin sharuda, ciki har da katse duk wata hulda ta kai tsaye da fadar gwamnati.  

Talla

A maimakon hulda da gwamnatin jihar, yanzu haka Sarkin zai rika hulda ne da karamar hukuma wadda za ta rika ba shi hatta izinin yin balaguro.

Tuni aka kafa kwamiti a matakin tarayya domin sasanta Sarki da Ganduje.

An kafa kwamitin ne karkashin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Abdulsalam Abubakar da zummar sulhunta rikicin tsakanin Ganduje da Sarkin na Kano.

Kazalika kwamitn ya kunshi gwamnoni jihohi biyu da suka hada da Kayode Fayemi na Ekiti da kuma Aminu Masari na Katsina.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Adamu Fika, Wazirin Fika da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da Alhaji Abdullahi Ibrahim da Dr. Dalhatu Sarki Tafida da Dr, Umaru Mutallab da Farfesa Ibrahim Gambari da Sheik Sharif Ibrahim Saleh da kuma Dr.adamu Fika.

A bangare guda, Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta Northern Elders Forum, ita ma ta fara wani zama na sulhunta shugabannin biyu a birnin Kano.

A yayin zantawasa da RFI, Dr. Hakeem Baba Ahamad, daya daga cikin dattawan da suka shiga tsakani, ya ce,  ba za su zura ido ba har Kano ta tsunduma cikin wani tashin hankalin da zai iya shafar daukacin arewacin Najeriya mai fama da tarin matsaloli.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren kalaman Baba Ahamad

Dr. Hakeem Baba Ahamad kan rikicin Kano

Tun bayan kammala zaben 2019 a Najeriya, aka fara takun-saka tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi, yayin da gwamnan ya kirkiri sabbin masarautu hudu masu daraja ta farko a jihar, lamarin da wasu ke dangantawa da yunkurin rage karsashin Sarki Sunusi.

Kodayake gwamnatin jihar ta ce, ta dauki matakin kirkirar masarautun ne domin ci gaban al'ummar Kano.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.