Gwamnatin Najeriya ta yi umarnin sakin Dasuki da Sowore
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci hukumar tsaro ta DSS ta saki tsohon mashawarcin shugaban kasa kan sha'anin tsaro zamanin mulkin Goodluck Jonathan wato Kanal Sambo Dasuki, tare da jagoran zanga-zangar RevolutionNow Omoyele Sowore.
Cikin wata sanarwa da babban mai shigar da kara na gwamnatin Najeriyar kuma ministan shari'a Abubakar Malami ya fitar a yau Talata, ya ce matakin sakin mutanen biyu na da alaka da umarnin da kotun kasar ta bayar.
Kanal Dasuki wanda ke tsare a hannun jami’an tsaron Najeriya fiye da shekaru 3 duk da mabanbantan umarnin kotunan kasar, a cewar Abubakar Malami, gwamnatin Najeriya ta mutunta umarnin kotunan kasar wajen baiwa hukumar ta DSS izinin sakinsu.
A bangare guda shima Sowore wanda tuni alkalin da ke sauraren kararsa ya sanar da janyewa, bayan da tun farko kotu ta yi umarnin sakinsa cikin kasa da sa'o'i 24 amma kuma DSS suka sake kama shi har cikin dakin shari'ar kotun Najeriyar Malami ya ce yanzu haka shima zai bar hannun jami'an na DSS.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya dai ta fuskanci suka da caccaka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam sakamakon rike Dasuki tsawon shekaru ciki har da kungiyar Amnesty International.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu