Najeriya

Baitulmalin Najeriya na barazanar karewa - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. REUTERS/Joe Penney

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayi gargadin cewa kasar na fuskantar barazanar karewar baitulmalinta, sakamakon karuwar adadin bashin da gwamnati ke karba.

Talla

Obasanjo yayi gargadin ne yayin halartar wani taron addini a birnin Legas, inda ya koka kan yadda Najeriya da kuma wasu kasashen Afrika ke ciwo bashi daga bankin duniya, asasun IMF da sauran hukumomi, matakin da tsohon shugaban ya ce idan ba’a yi taka tsantsan ba, zai tagayyara tattalin arzikinsu.

Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ja hankali kan kididdigar da ta nuna cewar, zuwa karshen watan Maris da ya gabata na 2019, adadin bashin da ake bin Najeriya a ketare ya kai dala biliyan 81 da miliyan 274.

Sai dai a nata gefen, gwamnatin Najeriya, ta sha kare kanta da cewar, tana karbo bashin ne, domin cike gibin bukatun gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da noma da kuma samar da ababen more rayuwa, da zummar cimma burin daina dogaro kan arzikin man fetur wajen samun kudaden shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI