Najeriya

Najeriya za ta janye sojojinta daga arewa maso gabas

Wasu daga cikin sojojin Najeriya
Wasu daga cikin sojojin Najeriya Pulse.ng

Rundunar Sojin Najeriya za ta fara janye dakarunta daga yankin arewa maso gabashin kasar nan da shekara mai kamawa kamar yadda babban hafsan sojin ruwa na kasar, Rear Admiral Ibok Ekwe-Ibas ya sanar jim kadan da kammala ganawarsu da shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

Talla

Mista Ekwe-Ibas ya ce, za a janye sojojin ne daga wasu yankuna na Najeriya nan da rubu’in sabuwar shekara domin mayar da hankalinsu kan wasu sabbin barazana da ke kunno kai, yayin da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence , za su maye gurbin sojojin.

Sai dai a yayin zantawa da RFI Hausa, Honorable Isa Lawan Kangar, tsohon dan Majalisar Dokokin Najeriya kuma tsohon shugaban Karamar Hukumar Guzamala, daya daga cikin yanki mai fama da rikicin Boko Haram a jihar Borno, ya ce, sam ba sa goyon bayan janye sojojin.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da shi

Hira ta musamman kan janye dakarun Najeriya daga yankin arewa maso gabas

Babban hafsan ya ce, akwai bukatar daukar wannan mataki na gwaji domin tabbatar da kwazon ‘yan sandan Najeriya da jami’an Civil Defence wajen kula da yankunan da suka hada da arewa maso gabashin kasar.

Ekwe-Ibas ya kara da cewa, sha’anin kula da tsaron cikin gida ya rataya ne a wuyan jami’an ‘yan sanda, yana mai cewa sojoji na kawo dauki ne da zaran al’amura sun rincabe wa ‘yan sandan, kuma muddin al’amuran suka daidaita, babu abin da ya ragewa sojojin illa ficewa domin bai wa ‘yan sandan ragamar ci gaba da kula da tsaro.

Babban jami’in ya tunatar da al’umar kasar shirin gwamnatin shugaba Buhari na daukar sabbin jami’an ‘yan sanda dubu 10 domin cike gurabe, yana mai fatan sabbin daukar za su samu cikakken horo.

A cewar babban hafsan, ba za su iya ci gaba da dankwafar da sojojin kasar wuri guda ba musamman ganin cewa, an cimma burin da ake fata a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Kodayake wasu bayanai na cewa, sai an tantance sha’anin tsaro kafin daukar matakin a arewa maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI