A Najeriya 'Yan bindiga sun kashe mutane 19 a jahar Kogi

Hoto mai nuna alamar 'yan bindiga a Najeriya
Hoto mai nuna alamar 'yan bindiga a Najeriya Jakarta Globe

‘Yan bindiga sun hallaka mutane akalla 19 a jihar Kogi ta Najeriya, inda suka kona gidaje da suka hada da fadar masarautar garin Tawari har ma da wasu wuraren ibada.

Talla

Wata mazauniyar yankin da ta tsira da ranta, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, a cikin daren da ya gabata ne maharan kimanin 100 suka dirar wa jama’ar garin na Tawari, inda kuma suka sace abinci a wasu gidaje.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kogi Mista Williams Anya, ya tabbatar da harin, inda yace, cikin gidajen da ‘yan bindigar suka kona har da gidan basaraken gargajiya na yankin.

Garin na Tawari na kan babban titin Lokoja zuwa Abuja babban birnin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.