Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta kashe mata dakaru 4 a Kaduna

Wasu daga sojojin Najeriya.
Wasu daga sojojin Najeriya. Reuters

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jami’inta guda kawai ya rasa ransa, yayin farmakin da ‘yan bindiga kimanin 70 suka kaiwa sojoji a Unguwan Yako dake Buruku akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jiya alhamis.

Talla

Kafin bayanin rundunar sojin saman dai, wata majiyar ta bayyana cewa sojoji 4 maharan suka halaka yayin farmakin tare da kone motocin jami’an tsaron da yammacin ranar alhamis.

Sai dai cikin jawabin da rundunar sojin saman Najeriya ta fitar, kakakinta Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce jami’insu 1 ne ya rasa ransa a lokacin da suka yi nasarar dakile mummunan farmakin da ‘yan bindigar suka shirya kaiwa kan yankin na Ungwan Yako.

Farmakin baya bayan nan ya zo ne kwanaki 2 bayan harin da wasu ‘yan bindigar suka kai kan wata makarantar horas da malaman addinin Kirista a unguwar Kakau dake jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.