Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a Zamfara da Katsina

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. AP/Lekan Oyekanmi
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Sojojin Najeriya dake rundunar Operation Hadarin Daji, sun sanar da halaka ‘yan bindiga sama da 100, yayin farmakin da suka kaddamar kan sansanonin maharan a dazukan kananan hukumomi 4 dake jihohin Katsina da Zamfara.

Talla

Sanawar da Captain Ayobami Oni-Orisan, kakakin rundunar ta Hadarin Daji ya fitar, ta ce sojin Najeriyar sun yi barin wuta kan ‘yan bindigar ne a kananan hukumomin Anka, Maru, Bukkuyum dake Zamfara, sai kuma Jubia a jihar Katsina, domin murkushe ragowar ‘yan bindigar da suka bijirewa shirin gwamnati na yi musu afuwa.

Sanawar kakakin sojin ta kara da cewar sun yi nasarar kwace makamai masu yawan gaske daga hannun ‘yan bindigar gami da ceto wasu mutane goma dake tsare a hannunsu.

Jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara, da kuma Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya sun shafe tswon lokaci suna fuskantar matsalolin tsaro na yin garkuwada mutane don karbar kudin fansa, da kuma satar dabbobi.

Sai dai a baya bayan nan an samu saukin hare-hare a sassan jihohin musamman Zamfara, sakamakon shirin yiwa ‘yan bindigar afuwa da karbe makamansu da gwamnati ke jagoranta, sai kuma tashi tsaye da jami’an tsaro suka yi wajen murkushe ragowar wadanda suka bijire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.