Najeriya

Yau Gwamna Tambuwal zai san makomarsa a Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. Daily Post Nigeria

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto da ke Najeriya ta ce, tana cikin shiri domin tabbatar da doka da oda yayin da a yau Litinin, kotun kolin kasar za ta yanke hukuncin karshe da zai fayyace ko waye halastaccen gwamnan jihar ta Sokoto tsakanin Ahmed Aliyu Sokoto na jam’iyyar APC wanda ya shigar da karar da kuma gwamna mai ci Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP.

Talla

Alhaji Aliyu Sokoto na kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na amincewa da nasarar da Aminu Tambuwal ya samu a zaben gwamnan da aka gudanar a bara.

An girke dubban jami’an tsaro a sassan kasar domin tabbatar da zaman lafiya a yayin da kotun kolin za ta yi zaman yanke hukuncinta.

Kwaminshinan ‘yan sandan jihar, Alhaji Ibrahim Kaoje ya ce, ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro domin bai wa al’umma damar gudanar da harkokinsu na kasuwanici cikin lumana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI