Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta haramta wata sabuwar runduna

Motocin sabuwar rundunar Amotekun da gwamnatin tarayya ta haramta a Najeriya
Motocin sabuwar rundunar Amotekun da gwamnatin tarayya ta haramta a Najeriya Premium Times Nigeria
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta haramta sabuwar rundunar tsaro da aka yi wa lakabi da ‘Amotekun’ wadda gwamnonin jihohin kudu maso yammacin kasar suka kafa domin samar da tsaro a yankinsu.

Talla

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar,  Lauyan Gwamnatin
Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ayyana rundunar a matsayin haramtacciya, lura da cewa, ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar ta 1999 a cewar sanarwar ta ranar Talata.

Ministan Shari’ar ya ce, babu wata gwamnatin jiha da take da ‘yanci ko kuma karfin kafa wata kungiya ko hukuma da sunan samar da tsaro a Najeriya.

Sai dai wasu rahotanni sun ce, al'ummar Yarbawa za ta kalubalanci matakin haramta rundunar.

Bangarori daban-daban sun yi ta cece-kuce kan rundunar tsaron ta ‘Amotekun’ wadda jihohin kudancin kasar suka ce za ta kawo karshen matsalolin tsaro da suka hada da satar mutane don karbar kudin fansa a yankin.

A ranar Alhamis din makon jiya ne gwamnonin suka kaddamar da soma aikin rundunar a birnin Ibadan na jihar Oyo, inda ta kunshi ‘yan sanda da mafarauta da jami’an sa kai na Vigilante da kuma ‘yan kungiyar Odua Peoples Congress.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.