Ali Kwara Azare kan hare-haren 'yan bindiga a sassan Najeriya

Sauti 04:01
Wasu manyan hanyoyin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga.
Wasu manyan hanyoyin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga. Information Nigeria

A Najeriya hare-haren ‘yan bindigar dake karuwa a sassan Najeriya musamman kan wasu manyan hanyoyi, ciki har da babbar hanya tsakanin Abuja da Kaduna, da kuma Kadunan zuwa Zaria a baya bayan nan, ya sanya masana sha’anin tsaro da sauran jama’a tofa albarkacin baki kan dalilan da suka haifar da matsalolin tsaron, zalika da matakan da ya kamata a dauka don kawo karshen lamarin.Ali Kwara Azare na daga cikin ‘yan Najeriyar da a shekarun baya, yayi suna wajen bada gagarumar gudunmawa wajen yakar miyagun laifukan fashi da makami da na ‘yan bindiga.Bayan kazamin farmakin da aka kaiwa ayarin mai martaba Sarkin Potiskum Alhaji Umaru Bubaram ne kuma Sashin Hausa na RFI ya tattauna da Ali Kwara kan matsalar hare-haren ‘yan bindigar dake kamari a wasu sassan Najeriya.