Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

‘Yan bindiga sun bude wuta kan tawagar Sarkin Potiskum

Wani bangare na hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Zaria a Najeriya.
Wani bangare na hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa Zaria a Najeriya. Pulse.ng
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 Minti

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun bude wuta kan tawagar motocin Sarkin Potiskum Alhaji Umaru Bubaram akan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Talla

Yayinda yake tabbatar da kai harin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya ce farmakin ‘yan bindigar masu yawan gaske, ya rutsa da tawagar Sarkin na Potiskum ne da sauran matafiya a kusa da Maraban Jos da misalin karfe 11 na daren ranar talata.

Wani da ya samu tsira da ransa ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewar kai tsaye ‘yan bindigar suka bude wuta kan tawagar Sarkin da sauran jama’a bayan tare hanyar, inda suka kashe mutane da dama da jikkata wani adadin mai yawa, ciki har da Dogaran Sarkin guda 4, da kuma wasu fasinjojin wata motar Safa.

Barista Abubakar Umar Bubaram da ne ga Mai Martaba Sarkin na Potiskum, ya shaidawa wakilinmu Bilyaminu Yusuf cewar mahaifin nasu ya tsira daga farmakin.

Barista Abubakar Umar Bubaram

Sai dai kakakin ‘yan sanda DSP Yakubu Sabo ya ce akalla mutane 6 ne suka mutu wasu biyar kuma suka jikkata a harin, yayinda kuma ‘yan bindigar suka yi awon gaba da adadi mai yawa matafiyan da suka rutsa, kafin isowar jami’an tsaro.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewar yanzu haka sun soma farautar ‘yan bindigar, tare da shan alwashin ceto jama’arda suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.