Najeriya

'Yan bindiga sun halaka mutane 31 a Zamfara

Wasu 'yan gudun hijira a Zamfara da 'yan bindiga suka tilastawa kauracewa muhallansu.
Wasu 'yan gudun hijira a Zamfara da 'yan bindiga suka tilastawa kauracewa muhallansu. RFI HAUSA

Rahotanni daga Zamfara a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 31 yayin farmakin da suka kai kashi 2 a ranar talatar da ta gabata.

Talla

‘Yan bindigar sun kai farmakin ne a kauyen Makosa dake karamar hukumar Zurmi inda suka halaka wasu jami’an lafiya 2 dake aikin bada rigakafin cutar Polio, yayinda kuma a kauyen Babban Rafi maharan suka kashe mutane 29.

Wani da ya tsira daga farmakin kauyen na Babban Rafi, ya ce da safiyar ranar talata 4 ga Janairun 2020, ‘yan bindigar suka kutsa kauyen tare da bude wuta kan jama’a.

Tuni dai kakakin ‘yan sandan Zamfara Muhammad Shehu ya tabbatar da harin, tare da karin hasken cewar, ‘yan bindigar da suka kai farmakin basa cikin wadanda suka rungumi shirin afuwa da ajiye makaman da gwamnati ke jagoranta.

Rahotanni dai sun ce farmakin ya tilastawa mazauna kauyen na Babban Rafi tserewa cikin dazuka, duk da haka kuma sai da ‘yan bindigar suka halaka wasu daga cikinsu bayan bin sawunsu cikin dazukan.

Hare-haren ‘yan bindiga a sassan Zamfara a baya bayan nan na zuwa ne bayanda kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Nagoggo a farkon watannan na Janairu, ya ce akalla mutane dubu 6 da 319 ‘yan bindiga suka halaka a jihar ta Zamfara cikin shekarar 2019 kadai.

A baya bayan nan ne kuma sojojin Najeriya suka bayyana nasarar halaka sama da 'yan bindiga 100 yayin farmakin da suka kaddamar kan sansanonin maharan a dazukan kananan hukumomi 4 dake jihohin Katsina da Zamfara, wadanda suka hada da Anka, Maru, da kuma Bukkuyum a Zamfara, sai kuma Jubia a jihar Katsina.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.