RFI Hausa

An kirkiri shafin RFI Hausa na bogi

Lallai Hukumar RFI Hausa na gargadin mutanen da ke wallafa labaran karya da sunan gidan rediyon da su yi hattara
Lallai Hukumar RFI Hausa na gargadin mutanen da ke wallafa labaran karya da sunan gidan rediyon da su yi hattara RFI Hausa

An kirkiri sabon shafin RFI Hausa amma na bogi a dandalin sada zumunta na Facebook, inda wannan sabon shafin ke wallafa labaran karya da sunan RFI Hausa.

Talla

Labarin karya na baya-bayan nan da shafin ya wallafa, shi ne na Maryam Sanda wadda Babbar Kotun Najeriya ta yanke mata hukuncin kisa bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello a birnin Abuja.

A labarin na karyar da aka wallafa a Facebook da sunan RFI Hausa, an ce wai Amnesty ta ce, ba za ta bari a rataye Maryam Sanda ba.

Taken labarin kamar yadda suka rubuta shi ne “ Baza mu bari a rataye Sanda ba. Inji kungiyar kere hakin Dan’adam.Amnesty."

RFI Hausa ta gaskiyar ba ta wallafa labari makamancin wannan ba. Sannan kuma Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty ba ta ce uffam ba game da hukuncin da aka yanke wa Maryam Sanda.

Tabbas mun wallafa labarin hukuncin da Kotun ta yi wa Maryam Sanda amma ba irin wannan na kanzon-kuregen ba.

Labarin da muka fara wallafawa da dumi-dumi a kan Maryam Sanda shi ne, mai taken 'Kotun Najeriya ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya',  kuma idan mai bibiyar mu ya latsa kan labarin kai tsaye zai kai shi cikin shafinmu na Intanet, inda zai karanta cikakken bayani.

Baya ga wannan, ba mu sake wallafa wani labari da ya danganci Maryam Sanda a shafinmu na Facebook ba.

RFI Hausa ta kuma gano cewa, wadannan mutane da suka kirkiri shafin na bogi na daukar labaranmu tare da wallafa su a shafin nasu.

YADDA ZA  A GANE RFI HAUSA NA BOGI

Da zaran an shiga shafinmu na RFI Hausa Facebook, za a ga wani karamin maki a cikin wata da’ira mai launin shudi a karkashin tambarin RFI Hausa daga gefen hannun hagu.

Wancan RFI Hausa na bogI, ba shi da wannan makin.

Sannan adadin masu bibiyar mu a shafinmu na Facebook sun zarce dubu 620.

Shi kuma shafin na bogi, dududu masu bibiyar su ba su wuce dubu 2 ba.

Kazalika shafinmu na gasken na dauke da hotunan bidiyo da dama da dubban mutane suka kalla, yayin da kuma yake dauke da hotunan barkwanci da muka saba wallafawa akai akai.

Lallai Hukumar RFI Hausa na gargadin mutanen da ke wallafa labarai da sunan gidan rediyon da su yi hattara!!!

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.