Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta rufe wani katafaren shago saboda Coronavirus

Jami'an Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki a Najeriya na bincike a katafaren shagon Panda da ke Abuja.
Jami'an Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki a Najeriya na bincike a katafaren shagon Panda da ke Abuja. Daily Trsut

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta rufe wani katafaren shagon hada-hadar kayayyakin cimaka da ke babban binirn Abuja sakamakon dari-darin barkewar cutar Coronavirus wadda ta hallaka mutane 132 a China.

Talla

Cutar Coronavirus mai kamanceceniya da annubar SARS ta fara bulla ne a wata kasuwar hada-hadar nau’ukan abincin ruwa da ke birnin Wuhan na China, kuma tuni ta bazu a wasu kasashen duniya.

Kodayake kawo yanzu ba a tabbatar da bullar cutar a Najeriya ba.

Katafaren shagon da gwamnatin ta rufe a yankin Jabi na Abuja mai suna Panda Supermarket, na sayar da kayayyakin da suka hada da barasa da kayan kwalama da kayayyakin kananan yara har ma da abincin ruwa dangin kifi da makamancinsa.

Hukumar da ke Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Najeriya ce ta rufe katafaren shagon bayan ta ce, bayanan da aka kwarmata mata sun nuna cewa, shagon ya yi safarar wasu nau’ukan abincin ruwa da dabbobi daga kasar China ta haramtacciyar hanya.

A cewar Hukumar, ta kuma gano wasu na’ukan abinci da wa’adin lalacewarsu ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.