'Yan bindiga na neman garin Gayari ya fanshi kanshi da miliyan 40

Bindigogin yaki kirar AK47
Bindigogin yaki kirar AK47 REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

A Najeriya ‘yan bindiga sun bai wa al’ummar garin Gayari na karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara zabin ko dai su biya tarar Naira miliyan arba’in su tsira da rayukansu ko kuma su hallaka ilahirin al’ummar garin.

Talla

Tuni dai hankalin al’ummar garin ya tashi bayanda ‘yan bindigar suka yi awon gaba da Sarkin garin tare da dan sa a daren ranar Alhamis.

A wata zantawarsu da sashen hausa na RFI al’ummar garin na Gayari sun nemi daukin gwamnati da jami’an tsaro don tseratar da rayukansu dana iyalansu daga barazanar ta ‘yan bindigar.

A Najeriya dai matsalolin tsaron musamman batun garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.