Najeriya-Amurka

'Yan Najeriya da wasu kasashe 5 ba za su shiga Amurka ba

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

A Juma’ar nan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aiwatar da haramta wa ‘yan Najeriya da wasu kasashe 5 shiga kasar, kari kan jerin kasashen da tun da farko aka kakaba wa wannan haramcin da ya janyo cece kuce.

Talla

Baya ga Najeriya, kasa mafi shahara a nahiyar Afrika, kasashen da abin ya shafa a baya bayan nan sune: Myanmar, Eritrea, Kyrgyzstan, Sudan da Tanzania.

Wata sanarwa daga gwamnatin Amurka ta ce wannan mataki ya biyo bayan rashin hadin kai daga kasashen da abin ya shafa game da musayar bayanai, tsaron kasa da sauransu.

A gefen taron tattalin arzikin da ya gudana a birnin Davos shugaba Trump ya sanar da aniyarsa ta kara yawan kasashen da ya haramta wa shiga Amurka.

Trump ya sha nanatawa yayin yakin neman zabensa cewa zai haramta wa Musulmai shiga Amurka, kuma da darewarsa karagar mulki ya fara cika wannan alkawari a watan Janairun shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.