Najeriya

Kotun Kolin Najeriya ta soke nasarar APC a Bayelsa

David Lyon na APC da Kotun Kolin Najeriya ta soke kujerarsa ta gwamnan Bayelsa
David Lyon na APC da Kotun Kolin Najeriya ta soke kujerarsa ta gwamnan Bayelsa premiumtimesng

Kotun Kolin Najeriya ta soke zaben da aka yi wa David Lyon na Jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Jihar Bayelsa saboda samun mataimakinsa da gabatar da bayanan karya ga Hukumar Zabe dangane da takararsa.

Talla

Alkalan kotun guda 5 a karkashin jagorancin Mai Shari’a Mary Odili suka yanke hukuncin soke zaben kamar yadda Mai Shari’a Ejembi Eko ya karanta.

Mai shari’a Eko ya bukaci Hukumar Zabe ta bai wa dan takarar Jam’iyyar PDP Diri Duoye takardar zama zababben gwamna, saboda shi ya zo na biyu a zaben da aka yi.

Sakataren Jam’iyyar PDP a Najeriya, Sanata Ibrahim Tsauri ya yaba wa alkalan da suka yanke hukuncin saboda jajircewar da suka yi wajen tsayawa kan gaskiya da kuma tabbatar da ita.

Tsauri ya ce, sun san cewar akwai alkalai na gari masu tsage gaskiya komi dacinta, kuma akwai matsorata wadanda ke shakkar yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.