Najeriya

Sojin Najeriya sun sallami tsoffin mayakan Boko Haram 137

Wasu tsoffin mayakan Boko Haram da aka sallama a can baya bayan sun tuba.
Wasu tsoffin mayakan Boko Haram da aka sallama a can baya bayan sun tuba. Daily Post

Rundunar Sojin Najeriya ta sallami tsoffin mayakan Boko Haram 137 da suka kammala samun horo a wata cibiya da ke kula da sauya masu tunani, wanda hakan zai ba su damar komawa a cikin al’umma don ci gaba da rayuwa. To sai dai al’umma sun fara nuna fargaba, saboda a cewarsu sallamar mutanen, na taimakawa wajen kara tabarbaewar  tsaro a jihohin Borno da Yobe. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton da Bilyamin Yusuf ya aiko mana daga Maiduguri.

Talla

Sojojin Najeriya sun sallami mayakan Boko Haram 137

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.