Najeriya-Tsaro

Najeriya: Yawan zunubanmu ya kawo rashin tsaro - Sultan

Sarkin Musulmi Saad Abubakar
Sarkin Musulmi Saad Abubakar Daily Trust/Nigeria

SarkinMusulmi a Najeriya Alhaji Saad Abubakar ya ce ta’addancin da rashin tsaro da suka addabi kasar hukunci ne daga Allah, sakamakon rashin biyayya da dokokinsa.

Talla

Yayin jawabinsa a taron lalubo mafita game da matsalar rikice rikice da suka addabi kasar a Abuja, sarkin Musulmin ya ce ‘yan Najeriya na aikata zunubi ta wajen kin yi biyayya ga koyarwar Alku’ani da Bible.

Sultan din, wanda ya samu wakilcin Sarkin Jiwa, Dr. Idris Musa, ya bayyana takaici kan yadda rashin tsaro ya yi wa kasar katutu, inda ya koka cewa yanzu ma lamarin ya kai inda har masu hannu da shuni na nesanta kansu da talakawa.

Ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su ci gaba da wa kasa addu’a don samun wanzuwar zaman lafiya da walwala.

Rashin tsaro ya yi wa Najeriya mai yawan Al’umma da suka kai kusan dubu dari 200 dabaibayi, inda ta’addanci, mastalar ‘yan bindiga da ta masu satar mutane don karbar kudin fansa suka zama ruwan dare musamman a arewacin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.