Najeriya

Buhari ya gaza wajen kare Najeria daga Coronavirus - PDP

Magoyabayan jam'iyyar adawar Najeriya PDP
Magoyabayan jam'iyyar adawar Najeriya PDP Premium Times

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya, PDP ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gazawa wajen daukar matakan da suka dace wajen hana shigar cutar coronavirus kasar.

Talla

Sakataren yada labaran Jam’iyyar Kola Ologbodiyan ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa manema labarai, inda yake cewa samun wani dan kasar Italia da ya shiga Najeriya da cutar, ya nuna cewar gwamnati bata damu da rayuwar jama’ar ta ba.

Jam’iyyar tace gwamnatin da ta damu da talakawan ta ba zata bari ana shiga kasar ta ba tare da bincike da kuma tantance baki ba, musamman wadanda suka fito daga kasashen da aka samu cutar.

Sanarwar ta kuma zargi gwamnatin Buhari da kasa yin komai wajen taimakawa Yan Najeriya da suka makale a China, inda cutar ke cigaba da lakume rayuka.

PDP tace Yan Najeriya su kama Buhari da jami’an gwamnatin sa muddin cutar coronavirus ta haifar da matsala ga rayuwar su, bayan kuncin da gwamnatin ta jefa su da ya shafi matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI