najeriya - coronavirus

Najeriya: An canza wa mai cutar COVID 19 asibiti

Wani mutum a Algeria sanye da mayanin ido don kariya daga cutar coronavirus
Wani mutum a Algeria sanye da mayanin ido don kariya daga cutar coronavirus RYAD KRAMDI/AFP

Hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun ce an sauya wad an kasar Italiyan nan da aka samu da cutar mura mashako ta coronavirus wajen jinya don samun kulawa mai inganci.

Talla

Dan kasar Italiyan da aka killace a asibitin kula da cututtuka masu yaduwa a garin Yaba da ke Lagos tun a ranar Juma’a, ya koka da rashin ingancin asibitin, kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar Lagos Akin Abayomi ya bayyana.

Kwamishinan ya ce yanzu haka an kai shi wani wuri da aka mai inganci da aka gyara da na’urar sanyaya daki.

A ranar Juma’a ne dai hukumomi a Lagos suka gano wani baturen Italiya da cutar mashako ta Coronavirus, lamarin da ya sa aka kai shi asibitin kula d cututtuka masu yaduwa na Yaba a Lagos.

Tuni ma gwamnatin kasar ta gano mutane 28 da mutumin ya yi mu’ammala da su, kuma yanzu haka an kama su su na killace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.