Najeriya

'Yan bindiga sun kai hari a Askira Uba

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar boko haram ne sun kai hari kauyen Rumirgo dake Askira Uba a Jihar Barno inda suka kasha mutane 10 da kona gidaje da kuma satar abinci.

Yan bindiga sun kai farmaki kan kauyen Rumirgo dake jihar Borno
Yan bindiga sun kai farmaki kan kauyen Rumirgo dake jihar Borno Jakarta Globe
Talla

Wani mazaunin Yankin Adamu Galadima ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar sun kai harin ne da misalign karfe 5 da rabi na yammacin jiya, dauke da motar da aka dorawa bindiga mai sarrafa kan sa, inda suke harbi kan mai uwa da wabi.

Peter Malgwui dake zama a kauyen ya tabbatar da Yan bindigar sun kashe mutane 10 da kona gidaje da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI