Ba za mu yi sulhu da 'yan bindiga ba- Nasir El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Malam Nasir El-Rufai ya ce, gwamnatinsa ba za ta tattauna da 'yan bindigar da ke hallaka jama’a ba, kuma babu wani shirin yi musu afuwa a jihar.
Wallafawa ranar:
A yayin wata ziyara a wasu kauyuka hudu da ke Karamar Hukumar Igabi da Giwa domin jajanta musu kan harin 'yan bindigar da ya hallaka mutane sama da 50, El- Rufai ya nemi gafarar jama’ar saboda gazawarsa ta kare su daga harin.
Gwamnan ya shaida wa mazauna yankunan cewa, ya ziyarce su ne domin neman gafarar rashin iya kare su baki daya, yayin da ya shaida musu cewar suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun takaita hare-hare.
El-Rufai ya ce, ya bai wa jami’an tsaro umurnin murkushe duk wasu 'yan bindiga domin hakkinsu ne su mika su wajen mahalicinsu tun da ba sa bukatar zaman lafiya.
Gwamnan ya ce, jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu, sai dai wani lokaci suna shan wahala wajen zuwa kauyuka da wuri saboda rashin hanyoyi masu inganci.
El Rufai ya yaba wa sojojin sama da na kasa da 'yan sanda da kuma jami’an DSS kan daukin da suke kai wa a duk lokacin da aka nemi taimakonsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu