Najeriya

Babu dan Najeriyar da ya kamu da Coronavirus- Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta ce babu wani mutum da ya kamu da cutar Coronavirus bayan dan kasar Italiyar da aka tabbatar yana dauke da ita a makon jiya.

Jami'an kiwon lafiya a Najeriya da ke yaki da Coronavirus
Jami'an kiwon lafiya a Najeriya da ke yaki da Coronavirus Quartz
Talla

Ministan Lafiya Osagie Enahire ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce an yi gwaje-gwaje da dama kan wadanda ake zaton sun kamu da cutar amma babu wanda aka samu yana dauke da ita.

Enahire ya ce, yanzu haka shi dan kasar Italiyar da aka gano yana dauke da cutar, yana can  killace a cibiyar da aka ware domin kula da masu dauke da cutar da ke Yaba a Lagos, inda ake kula da shi.

Ministan ya ce, tuni aka gano mutane 19 a Jihar Lagos da 39 a Jihar Ogun wadanda suka yi mu’amala da baturen na Italiya da ya shiga kasar da cutar, kuma ana sa ido a kansu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi al’ummar kasar da su kauce wa yada labaran karya da zai tada hankalin jama’a game da cutar, yayin da ya ce, gwamnati na daukar matakan da suka dace wajen ganin ba a sake samun wani mai dauke da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI