Najeriya

Kotun koli ta dage zamanta kan zaben Zamfara

Kotun Kolin Najeriya ta sanar da dage hukuncin da ake saran zata yanke yau kan sake dube zaben Jihar Zamfara da aka yi ranar 9 ga watan Maris din bara zuwa ranar 17 ga watan nan.

Harabar Kotun Kolin Najeriya.
Harabar Kotun Kolin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Shugaban kotun Mai Shari’a Tanko Muhammed dake jagorancin alkalai 5 dake sauraron karar, yace an dage yanke hukuncin ne domin baiwa lauyan Jam’iyyar APC Robert Clark damar daidaita takardun sa.

Bangaren Jam’iyyar APC dake tare da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya shigar da sabuwar kara inda yake bukatar kotun kolin da ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke ranar 25 ga watan Mayun bara, wanda yayi watsi da kuri’un da Jam’iyyar ta samu a zaben da ya gudana da kuma bada umurnin rantsar da Yan takarar Jam’iyyar PDP a matakan Jiha da Majalisun Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI