Najeriya

MURIC ta bukaci hukunta masu watsi da kananan yara

Wasu kananan yara da manya da jami'an tsaro suka ceto a yankin Sabon Gari, dake karamar hukumar Daura a jihar Katsina, Najeriya.
Wasu kananan yara da manya da jami'an tsaro suka ceto a yankin Sabon Gari, dake karamar hukumar Daura a jihar Katsina, Najeriya. REUTERS/Stringer

Kungiyar dake kare hakkin Musulmi a Najeriya ta MURIC ta bukaci gwamnatin kasar da tayi dokar da za’a dinga hukunta iyayen da suka yi watsi da yaran da suka haifa suna gararamba a tituna.

Talla

Shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola yace samar da doka zata bada damar hukunta irin wadannan iyaye dake watsi da yaran da suka Haifa ganin yadda yawan s uke karuwa a tituna.

Akintola yace yara da da babban matsayi a cikin al’umma kuma goya su ta hanya mai kyau wajen basu tarbiya ta gari da ilimi shi ke daga darajar kasa.

Shugaban kungiyar ya bukaci Majalisar dokoki ta kasa da na Jihohi da su kaddamar da shirin samar da dokar da zata bada damar hukunta iyayen da suka yi watsi da hakkin da Allah Ya dora musu wajen kula da yaran.

Hukumomin Najeriya sun ce akalla yara miliyan 10 ke gararamba a tituna ba tare da zuwa makaranta ba, kuma akasarin su sun fito ne daga yankin arewacin kasar.

Masana sun ce rashin kula da irin wadannan yara ke baiwa bata gari damar amfani da su suna aikata manyan laifuffuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.