Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun halaka mutane 51 a wasu kauyukan Kaduna

Rahotanni daga Kaduna a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun halaka akalla mutane 51, yayin farmakin da suka kaiwa wasu kauyuka dake karamar hukumar Igabi.

'Yan bindiga sun kai hare-hare kan wasu kauyukan jihar Kaduna.
'Yan bindiga sun kai hare-hare kan wasu kauyukan jihar Kaduna. Information Nigeria
Talla

Wadanda suka samu tsira daga farmakin, sun ce jim kadan bayan kammala Sallar Asubahi ranar lahadin da ta gabata, maharan suka afkawa kauyukan da suka hada da Marina, Kerawa da kuma Zareyawa.

Yayin harin, ‘yan bindigar sun kone gidaje da dama gami da sace kayayyakin abinci.

Yayin zantawa ta jaridar Daily Trust dake Najeriya, Kansilan mazabar Kerawa, Malam Dayyabu Kerawa yace labarin kazamin farmakin bai bayyana da wuri ba saboda rashin kyawun layukan sadarwa a kauyukan da lamarin ya shafa.

Malam Dayyabu ya kara da cewar tuni aka yi jana’izar wadanda maharan suka halaka da yammacin ranar ta lahadi.

A nata bangaren rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta hannun kakakinta ASP Mohammed Jalige ta bayyana samun rahoton kai farmakin, sai dai tace labarin bai iso gareta akan lokaci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI