Boko Haram na mika kansu ga sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya tace ana cigaba da samun mayakan kungiyar Boko Haram dake mika kan su ga dakarun dake aiki a karkashin rundunar Lafiya Dole dake Maiduguri.

Wasu tubabbun mayakan Boko Haram.
Wasu tubabbun mayakan Boko Haram. Daily Post
Talla

Jami’in yada labaran sojin dake kula da ayyukan soji Kanar Aminu Ilyasu yace an samu karin mayakan da suka mika kan su ga dakarun gwamnati.

Kanar Ilyasu ya kuma bayyana cewar, dakarun su na cigaba da samun galaba akan mayakan a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da suka hada da Borno da Adamawa.

Jami’in yace dakarun su sun yi nasarar murkushe mayakan boko haram da suka nemi kutsa kai karamar hukuma Madagali dake Jihar Adamawa, inda suka kasha 3 kana sauran suka tsere dauke da harin bindiga.

Kanar Ilyasu ya kuma bayyana kubutar da wata mata da ‘dan ta da sojoji suka yi a Ngoshe dake karamar hukumar Gwoza a Jihar Barno bayan kwashe shekaru 2 a hannun su.

Jami’in yayi kuma bayani kan nasarorin da suka samu a Baga da Dogon Baga dake karamar hukumar Kukawa a Jihar Barno da kuma tarin makaman da suka kwace daga hannun mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI