Boko Haram ta dirar wa sojojin Najeriya da asuba
Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa, mayakan Boko Haram sun kashe mutane da dama da suka hada da jami'an tsaro a wani farmakin ba-zata da suka kai sansanin sojin kasar a sanyin safiyar wannan Larabar.
Wallafawa ranar:
Mayakan sun taso ne daga Gwoza Kalla domin kai harin a kan dakarun kasar da ke garin Damboa da misalin karfe 5:30 na asuba agogon Najeriya,inda suka yi ta ruwan harsashai kan sansanin.
Wani ganau ya ce, mayakan sun yi amfani da manyan motocin yaki guda biyu, yayin da suka yi ta harbe-harbe lokaci zuwa lokaci.
Bayanai na cewa, an shafe tsawon sa’o’i biyu ana dauki-ba-dadi da mayakan na Boko Haram.
A yanzu dai hankula sun kwanta, amma tuni jama’a da dama suka tsere zuwa garin Chibok don samun mafaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu