Najeriya

Majalisar Najeriya na shan caccaka saboda Coronavirus

‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya na shan caccaka kan matakin da suka dauka na dakatar da zamansu har tsawon makwanni biyu saboda hana yaduwar cutar Coronavirus a zauren Majalisar Tarayyar Kasar.

Zauren Majalisar Wakilan Najeriya
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya
Talla

Kungiyoyin fararen hula na kasar sun caccaki matakin da suka ce, ya saba wa ka’ida.

Darektar Cibiyar Kare Democradiya da Ci Gaban Al’umma CDD, Idayat Hassan ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, majalisar ba ta da hujjar daukar wannan matakin saboda a cewarta, mutun daya kacal aka tabbatar yana dauke da cutar a jihar Lagos.

Hassan ta diga ayar tambaya, tana mai cewa, shin majalisar za ta dakatar da kanta har abada da zaran an tabbatar da sabbin mutanen da cutar ta harba nan da ‘yan makwanni masu zuwa? Abin kunya ne abin da suka yi. Inji ta.

Babu wata Majalisar Dokoki a fadin duniya da ta dakatar da ayyukanta saboda fargabar Coronavirus kamar yadda Hassan ta yi karin bayani.

Shi ma Darektan Cibiyar Kare Hakkin Bil’adama da Bunkasa Ilimin Al’umma CHRICED, Dr. Ibrahim M. Zikirullahi, ya ce, babu mutun guda da aka tabbatar dauke da Coronavirus a Abuja, sannan ba a samu cutar ba a zauen Majalisar, ballantana a fake da wannan hujjar har a dakatar da ayyukanta.

Majalisar Wakilan ta ce, ta dauki matakin ne domin bai wa mambobinta damar gwajin cutar tare da daukar matakan hana bazuwar ta a Majalisar Tarayyar.

Idem Uyinan na jam’iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom ya fara gabatar da kudirin daukar matakan gaggawa wajen tunkarar Coronavirus a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI