Najeriya

Masu neman kujerar shugaban kasa ke min zagon-kasa- Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Adams Oshiomhole da ke fuskantar barazanar raba shi da mukaminsa sakamakon korar sa da a ka yi daga mazabarsa ta Jihar Edo da kuma dakatar da shi da wata kotu ta yi a Abuja, ya tattauna da RFI Hausa bayan ganawar da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa, matakin da ke zuwa bayan wata kotu a Kano ta jingine umurnin kotun Abuja. 

APC Chairman Adams Oshiomhole and president Muhammadu Buhari of Nigeria
APC Chairman Adams Oshiomhole and president Muhammadu Buhari of Nigeria RFI Hausa
Talla

Oshiomhole ya yi zargin cewar, wasu masu neman takarar shugaban kasa da wasu gwamnoni guda 3 ke neman ganin an raba shi da mukaminsa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya yi da Oshiomhole jim kadan da ganawarsa da Buhari a Abuja.

Masu neman kujerar shugaban kasa ke min zagon-kasa- Oshiomhole

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI