Kano ta fara tura almajirai jihohin su

Wasu almajirai a Najeriya
Wasu almajirai a Najeriya tribuneonlineng.com

Gwamnatin Jihar Kano dake Najeria tace ta fara kama almajiran dake bara a Jihar tana mayar da su Jihohi da kasashen da suka fito sakamakom dokar da tayi na hana bara a fadin jihar.

Talla

Mai magana da yawun Hukumar Hisbah da aka dorawa alhakin aiwatar da dokar, Lawan Fagge ya shaidawa manema labarai cewar tuni aka kama almajirai sama da 1,500 aka kai su Jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Borno da kuma Yobe.

Fagge yace sauran sun hada da wadanda suka fito daga Jihar Kanon kan ta da Adamawa da kuma kasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Jami’in yace daga cikin almajiran da aka kama ‘yan Jihar Katsina sun fi yawa sai kuma wadanda suka fito daga Jihar Jigawa ne mafi karanci.

Fagge yace daga cikin almajiran da aka kama kashi 70 yara ne kanana masu shekaru tsakanin 7 zuwa 12, yayin da sauran kuma mata ne masu yawan shekaru wadanda suka mayar da bara ta zama sana’a.

Gwamnatin Kano dai ta kaddamar da shirin ingannta harkar bada ilimi wanda zai bada damar hada karatun boko da na addinin Islama da aka fi sani da karatun allo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.