Babu wani da ya sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya

Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya
Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya Quartz

Gwamnatin Najeriya tace babu wani Karin mutum da ya kamu da cutar coronavirus a fadin kasar bayan dan kasar Italian da aka samu a makon jiya.

Talla

Ministan lafiya Osagie Ehanire yace ana cigaba da sa ido da kuma kula da dan kasar Italian a Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa dake Lagos kuma yana samun sauki sosai.

Ehanire ya bayyana cewar ana kuma sanya ido kan mutane 21 a Jihar Lagos da wasu 40 a Jihar Ogun da suka yi mu’amala da dan kasar Italia kuma har ya zuwa yau babu wanda ya nuna alamar kamuwa da ita.

Ministan yace daga cikin fasinjoji 148 da suka isa Najeriya tare da dan kasar Italian an gano 55 kuma jami’an kula da lafiya na sanya ido akan su.

Ehanire ya baiwa Yan Najeriya shawara da su kaucewa yada bayanan karya, yayin da gwamnati ke daukar duk matakan da suka dace wajen dakile yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.