'Yan sanda sun kubutar da Mata da Jarirai a Ogun

‘Yan sanda a Najeriya sun kubutar da mutane 13 daga wani gina da aka tara mata dimin haifa jarirai da ake sayar wa jama’a a cikin wani gari da ke jihar Ogun.

‘Yan sanda a Najeriya sun kubutar da mutane 13 daga wani gina da aka tara mata dimin haifa jarirai da ake sayar wa jama’a a cikin wani gari da ke jihar Ogun.
‘Yan sanda a Najeriya sun kubutar da mutane 13 daga wani gina da aka tara mata dimin haifa jarirai da ake sayar wa jama’a a cikin wani gari da ke jihar Ogun. DIBYANGSHU SARKAR / AFP
Talla

‘Yan sanda sun ce mata 12 wadanda shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 25 a duniya tare da wani karamin jinjiri ne aka ‘yantar daga wannan gida.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya ce tabbas an tara matan domin haifa jariran da ake sayarwa, kuma tuni aka kama wanda ya mallaki gidan da kuma wasu mutane biyu da ake zargin cewa su ne suka tara matan domin yin kasuwanci da su.

Gano irin wadannan gidaje da ake tara mata don haifa jarirai domin sayarwa, ba sabon zace ba ne, domin ko a cikin makon jiya ‘yan sanda sun ‘yantar da jarirai 24 da kuma mata 4 a garin Port Hacourt da ke kudancin kasar.

Bayanai na nuni da cewa ana sayar da irin wadannan jarirai a kan farashin da ya kama daga Naira dubu 500 zuwa sama, wato kwatankwacin dalar Amurka dubu daya da 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI