Najeriya

Najeriya ta ware naira miliyan 984 don yakar annobar Coronavirus

Ma’aikatar lafiyar Najeriya ta ce gwamnatin kasar ta mika mata naira miliyan 620 domin yakar annobar murar Coronavirus da zuwa yanzu ta bulla a kasashe sama da 90.

Wani misalin fasalin kwayar cutar murar mashako ta coronavirus da masana kimiyya suka fitar.
Wani misalin fasalin kwayar cutar murar mashako ta coronavirus da masana kimiyya suka fitar. MAM/CDC/Handout via REUTERS
Talla

A halin yanzu dai gwamnatin Najeriya ta ware jimillar kudi naira miliyan 9 da 84 kenan domin yakar annobar, bayan bada kashin farko na naira miliyan 3 da 64.

Ranar 24 ga Fabarairun da ya gabata, aka tabbatar da bullar cutar ta Corona a Najeriya, bayan gano wani dan Italiya daya kamu da ita.

A haliin da ake ciki, ministan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yace jami’ai na kan kokarin gano ragowar fasinjoji 93 da suka shiga jirgi guda da mutumin da ya fara shigar da cutar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI