Legas ta sa ido kan baki sama da 300 saboda Coronavirus
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Legas a Najeriya, ta ce yanzu haka tana sa idanu kan akalla mutane 349 da suka yi tattaki zuwa jihar daga kasashe daban daban, saboda cutar Coronavirus.
Ma'aikatar lafiyar jihar ta Legas ta ce baki dayan mutanen dake karkashin sa idon sun fito ne daga kasashen da annobar murar ta Coronavirus ta yi karfi.
Cibiyar lura da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce tana bukatar naira biliyan 1 da miliyan 600 don yakar annobar murar ta Corona, daga ciki kuma kawo yanzu gwamnatin tarayyar kasar ta mika mata naira miliyan 984.
Yanzu haka dai bayaga Najeriya, kasashen Afrika da suka tabbatar da bullar annobar murar cikinsu sun hadada Masar, Algeria, Afrika ta Kudu, Senegal, Kamaru, da kuma Togo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu