Najeriya

Najeriya ta sake darewa kan shugabancin lura da dakarun MDD

Zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Reuters/Brendan Mcdermid

Najeriya ta sake darewa kan shugabancin kwamitin majalisar dinkin duniya na musamman dake lura da ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Talla

Wakilan kasashe sun kadawa Najeriya kuri’ar ce a Juma’ar nan da ta gabata a shelkwatar majalisar dinkin duniyar dake birnin New York.

Karo na 48 kenan kasashe ke zabar Najeriya ta shugaban kwamitin na musamman tun daga shekarar 1972, wanda aka dorawa alhakin kula da ayyukan dakarun majalisar dinkin duniya sama da dubu 100 da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da kuma fararen hula kwararru daga kasashe 125, da ayanzu haka ke aiki a yankuna ko kasashe 14.

Najeriya ce ta 15 a duniya cikin jerin kasashen da suka fi baiwa majalisar dinkin duniya gudunmawar dakaru, ita ce kuma ta 8 a Afrika, bayanda a 2016 ta miak jimillar jami’ai dubu 2 da 170, da suka hada da sojoji dubu 1 da 721, ‘yan sanda 403, da kuma kwararru kan sha’anin tsaro 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI