Najeriya

Coronavirus ta kama dan Najeriya a Amurka

Jami'an yaki da cutar Coronavirus
Jami'an yaki da cutar Coronavirus Thomas SAMSON / AFP

Hukumomin birnin Washington DC da ke Amurka sun ce, wani dan Najeriya da ya ziyarci kasar ya kamu da cutar Coronavirus kamar yadda gwajin da aka yi masa a wani asibiti da ke Maryland ya nuna.

Talla

Mai rike da kujerar Magajin Garin birnin , Muriel Bowser ta ce mutumin ya dauki lokaci a Washington bayan ziyarar da ya kai daga Najeriya inda yake zaune da ‘yan uwansa.

Jami’ar ta ce, sun tabbatar da kamuwar mutane biyu a Washington, wato dan Najeriyar da kuma wani mazaunin birnin.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce, babu alamar cewa, dan wasan ya kamu da kwayar cutar ce  daga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.